Jami'an FRSC sun kashe abokin aikinsu da zai musu tonon silili

Jami'an FRSC sun kashe abokin aikinsu da zai musu tonon silili

Wani jami'in hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC, ya mutu a daren ranar Alhamis sakamakon makurra da ya sha hannun abokan aikinsu biyu a garin Onitsha da ke jihar Anambra.

An kashe marigayin, Emeka Ojei ne saboda ya yi yunkurin tona asirin rashawa da daya daga cikin wadanda suka kashe shi ya aikata a ofis.

The Nation ta gano cewa marigayin ya gama tattara bayanai kan rashawa da ya ke shirin zuwa ya yi rahoto a hedkwatan hukumar da ke Benin gabanin kashe shi.

DUBA WANNAN: Bukola Saraki kaman Abacha ya ke - Sanatan PDP

Wani ma'aikacin hukumar da ya yi hira da The Nation amma ya bukaci a sakaya sunansa ya ce wanda ake zargi da kisan ya gargadi marigayin kada ya tona masa asiri amma rashin amincewa da hakan ne ya tilasta masa kashe shi.

Ya ce jami'in da aka kashe yana kokarin karbar wayar salularsa daga hannun daya daga cikin wadanda ake zargi da kisar sai yayin da na biyu ya makure masa wuya har sai da ya ce ga garinku.

Ya ce, "Emeka yana daya daga cikin jami'an mu da ke aiki kan wani rahoto na rashawa da za a aika hedkwata da ke Benin.

"Yana shirin tafiya kai rahoton ne sai mai gidansa ya kira shi ya bukaci ya fasa zuwa amma bai amince da hakan ba.

"Mai gidansa yana kokarin karbar wayansa yayin da dayan jami'in ya makure masa wuya daga bayansa. Yana kokowa da su kan wayar ne har sai da suka kashe shi."

Majiyar Legit.ng ta gano cewa an shigar da kara ofishin 'yan sanda da ke yankin kuma an kama wadanda ake zargi.

Kakakin FRSC na jihar, Pascal Anigbo ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel