Da yiwuwa za a dakatar da Sanusi bayan ya amsa tuhumar Ganduje – Majiya tayi ikirari

Da yiwuwa za a dakatar da Sanusi bayan ya amsa tuhumar Ganduje – Majiya tayi ikirari

Da yiwuwa a dakatar da sarki Muhammadu Sanusi na Kano bayan mayar da martani akan korafin da gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya aika masa, bisa zargin kashe kudade ba bisa ka’ida ba.

Wata majiya wacce tayi magana da jaridar The Cable ta bayyana cewa maiyiwuwa a dakatar da sarkin bayan ya mayar da martani ga tuhumar da ake masa.

Gwamna Ganduje ya soma daukar mataki akan Sanusi ne a watan Mayu tare da zarge-zargen cewa yana shirin tsige sarkin bisa rashin goya mishi baya a yakinsa na neman zabe a karo na biyu.

Mako guda bayan rahoton, Gwamna Ganduje ya sa hannu a dokar raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar yayinda hukumar yaki da rashawa ta jihar ta sake rayar da bincikin masaurautan a karkashin Sanusi.

Bayan bincikenta, hukumar yaki da rashawan ta fito da shawarwarin dakatar da sarkin, inda take cewa ta gano an kashe kudi naira biliyan 3.4 a masarautan a karkashin Sanusi.

An tattaro cewa an kashe kudaden ne ba bisa ka’ida ba a tsakanin 2014 da 2017.

Biyo bayan shawarar hukuman yaki da rashawan ne Gwamna Ganduje ya aika takardar neman ba’asi zuwa ga sarkin.

Ofishin Sakatare gwamnatin jiha ce ta aika da wasikar a madadin gwamnan.

Munir Sanusi, shugaban ma’aikatan sarkin Kano, ya tabbatar da karbar wasikar, inda yake cewa an bukaci sarkin ya mayar da martani cikin sa’o’i 48.

Yace masarautan na nazari akan abubuwan da korafin da aka aiko ma masaraken ya kunsa.

Wasikar yana zuwa ne yan kwana biyu bayan shi da Ganduje sun yi musabaha da kuma sallah Eid-il- Fitr tare.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: CCB ta saki sunayen sanatocin da za a bincika (jerin sunayen) Read

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, yace duk abunda Sanusi ya aikata na kurakurai, yana neman gwamnatin jihar ta sassauta masa ba tare da daukan mataki mai “tsauri” ba akan sa.

Sarki Danyaya ya nuna ra’ayinsa ne bisa sabbin masarautu hudu da aka karkiro daga masarautar Kano kwanan nan, wanda hakan yana iya rage daraja da kuma ikon Sanusi.

Sarkin Ningi ya bukaci yan siyasa da gwamnatoci dasu kasance masu juriya da hakuri wajen hukunta sarakuna masu laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel