Da zafinsa: Rabuwar kawuna tsakanin Gwamnoni yayin ganawa da Buhari

Da zafinsa: Rabuwar kawuna tsakanin Gwamnoni yayin ganawa da Buhari

- Maganar kirkiro yan sandan jiha ta janye rabuwar kai a tsakanin gwamnoni yayin da suke ganawa da Shugaba Buhari a Villa

- Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ne ya sanar da manema labarai cewa an fara tattauna maganar amma ba'a cinma matsaya guda ba saboda kawuna sun rarrabu a tsakanin gwamnoni

Gwamnonin jihohi 36 sun rarrabu a kan batun fito da ‘yan sandan jiha da kuma na kananan hukumomi a lokacin da suke ganawa da shugaban kasa.

Ganawar wacce take ta sirri ta kammala yanzu nan tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohi 36 a fadar shugaban kasar dake Abuja.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti Dakta Kayode Fayemi ne ya shaidawa wakilin fadar shugaban kasa na jaridar Punch cewa an kasa maganar kirkirar yan sandan jiha a faifai amma ba’a samu matsaya guda ba daga wurin gwamnoni.

Wannan kuwa ya kasance ne saboda karfin jihohin ba daya bane, yayinda wasu jihohin keda kudin da zasu iya yin wannan abu sauran basu dashi.

KU KARANTA: Mafi karancin albashi: Gwamnonin PDP sun shirya biyan N30,000

Kudurin kirkirar yan sanda jiha na daga cikin kudurorin kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan binciken keta haqqin dan adam da dakarun SARS keyi.

An kuma kammala wannan bincike wanda aka baiwa Buhari rahotonsa a makon da ya gabata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel