Yanzu Yanzu: Babbar kotun tarayya ta yi umurnin bude tashoshin AIT da Ray Power

Yanzu Yanzu: Babbar kotun tarayya ta yi umurnin bude tashoshin AIT da Ray Power

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja tayi umurnin sake bude tashoshin African Independent Television (AIT) da na Ray Power FM.

Da yake yanke hukunci, Justis Ekwo Inyang ya umurci bangarorin da su ci gaba da kasancewa a yadda suke a ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu lokacin da aka ta

Justis Ekwo ya bukaci bangarorin da su bayyana a gaban kotu a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuni domin shari’a.

A ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni ne hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talbijin ta Kasa (NBC), ta janye lasisin yada labarai na Kamfanin Daar Communications Ltd.

Kamfanin Daar Communications, mallakar Raymond Dokpesi, su ke da gidan talbijin na AIT da kuma Gidan Radiyon Ray Power a fadin kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: CCB ta saki sunayen sanatocin da za a bincika (jerin sunayen)

Babban Daraktan NBC, Modibbo Kawu ne ya sanar da wannan dakatarwa a Abuja, a lokacin da ya ke wa manema labarai jawabi.

Sakataren hukumar ta NBC, Muhammad Mujtaba Sada, ya bayyana cewa hukumar ta sha bai wa kafar watsa labaran shawarwari kan yadda take gudanar da ayyukanta wadanda suka saba wa kundin tsarin watsa labarai na kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel