Yanzu Yanzu: Kotu ta soki INEC, ta bukaci a ba Okorocha takardar shaidar cin zabe

Yanzu Yanzu: Kotu ta soki INEC, ta bukaci a ba Okorocha takardar shaidar cin zabe

- Wata kotun tarayya da ke Abuja ta soke hukuncin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na kin ba tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha takardar shaidar cin zabensa

- Kotu tace Baturen zabe ne kadai ke da hurumin kaddamar da mutum a matsayin wanda ya lashe zabe

- Ta bukaci INEC ta ba Okorocha takardarsa domin hukuncinta baya bisa ka'ida

Wata kotun tarayya da ke Abuja ta soke hukuncin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na kin ba tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha takardar shaidar cin zabensa a matsayin zababben sanata.

Kotun ta bayyana cewa hukuncin hana Mista Okorocha takardar cin zabensa ya saba ma doka don haka hukunci ne da baya bisa ka’ida.

A cewar kotun karkashin jagorancin Justis Okong Abang, baturen zaben hukumar INEC ne kadai ke da ikon kaddamar da mutum a matsayin mai nasara.

Mista Abang yace duk mutumin da baturen zabe ya kaddamar a matsayin wanda ya lashe zabe toh yana nan akan matsayinsa har sai masu kara sun yi nasarar soke kaddamarwar a kotun zabe.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: CCB ta saki sunayen sanatocin da za a bincika (jerin sunayen)

Kotun ta kuma zartar da cewa Mista Okorocha bai da matsala kasancewa shine ya shigar da kara kotun zaben.

Abang ya zartar da cewa kotun tarayya na da ikon yanke hukunci kan lamarin, inda ya bayyana hukuncin INEC a matsayin ba bisa doka ba kuma abun sokewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel