Da zafi-zafi: Buhari, gwamnoni da shugabannin tsaro na cikin ganawar sirri

Da zafi-zafi: Buhari, gwamnoni da shugabannin tsaro na cikin ganawar sirri

A yanzu haka wata ganawa na gudana a tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da gwamnonin jihohi 36 da shuwagabannin hukumomin tsaro a fadar shugaban kasa, Abuja.

Ganawar ya samu halartan mataimakin shugaban kasa Yemi Obasanjo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, da kuma shugaban ma’aikata, Abba Kyari, inda za su tattauna akan lamarin tsaro a kasar.

Gwamnonin da suka hallara sun hada da na Adamawa, Borno, Taraba, Kebbi, Delta, Sokoto, Imo, Ebonyi, Kogi, Yobe, Gombe, Ekiti, Lagos, Jigawa, Bauchi, Kano da Niger.

Da zafi-zafi: Buhari, gwamnoni da shugabannin tsaro na cikin ganawar sirri

Da zafi-zafi: Buhari, gwamnoni da shugabannin tsaro na cikin ganawar sirri
Source: UGC

Sauran sun hada da gwamnonin Anambra, Kaduna, Nasarawa, Plateau, Osun, Rivers, Oyo, Akwa Ibom, Zamfara, Kwara, Ondo, Bayelsa da Enugu.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ma ya halarci taron.

Da zafi-zafi: Buhari, gwamnoni da shugabannin tsaro na cikin ganawar sirri

Da zafi-zafi: Buhari, gwamnoni da shugabannin tsaro na cikin ganawar sirri
Source: UGC

Shuwagabannin tsaron da suka halarci taron sun hada da shugaban Ma’aikatan Tsaro, Gabriel Olonisakin, Shugaban sojoji, Tukur Buratai, shugaban sojin ruwa, Ibok Ekwe Ibas da shugaban hafsoshin sama Abubakar Sadique.

KU KARANTA KUMA: Ka tuna mulki na dan lokaci ne, mai karewa ne – Shehu Sani ya roki Ganduje

Da zafi-zafi: Buhari, gwamnoni da shugabannin tsaro na cikin ganawar sirri

Da zafi-zafi: Buhari, gwamnoni da shugabannin tsaro na cikin ganawar sirri
Source: UGC

Sauran sun hada da mai bada shawara akan harkar tsaron kasa, Babagana Monguno; Babban Darektan hukumar liken asiri na kasa, Ahmed Abubakar, sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu da Babban Darektan hukumar tsaro na sirri, Yusuf Bichi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel