Majalisa ta 9: An hana ‘yan jarida daukan kaddamar da sabuwar majalisar dokoki

Majalisa ta 9: An hana ‘yan jarida daukan kaddamar da sabuwar majalisar dokoki

- An dakatar da akasarin 'yan jaridu daga halartar zabe da kuma bikin kaddamar da sabbin yan majalisar dokokin Najeriya wanda za'a yi ranar Talata dake tafe

- Hukumar gudanarwa ta majalisar dokokin ce ta bada wannan sanarwa inda cikin yan jarida 80 da suke nemi damar yin wannan aiki 11 kawai aka bai wa izini

Hukumar gudanarwa ta majalisar dokokin Najeriya ta hana ‘yan jarida izinin shiga farfajiyar majalisar domin daukan hotuna yayin kaddamar da Majalisa ta 9.

Daga cikin ‘yan jarida 80 da aka tantance domin daukan hotuna a bangaren majalisar wakilai 11 ne kadai aka ba izinin shiga a ranar da za’a kaddamar da sabuwar majalisa.

Kazalika matsalar duk guda ce a bangaren majalisar dattawa inda da dama daga cikin ‘yan jaridan aka hana su izinin shiga majalisar domin zaben shugabanni da kuma kaddamarwa wacce za’ayi a ranar Talata mai zuwa.

Jerin sunayen yan jaridan da aka tantance ya zo hannun jaridar The Cable a ranar Alhamis, a al’adance yadda aka saba yi shine yan jaridan dake aiki tare da majalisar dokoki sune za suyi aikin ranar kaddamar da sabuwar majalisar.

Kaddamarwa ta majalisa ta 7 da 8 duk ba a samu irin wannan matsalar ba. Abinda ke shirin faruwa a yanzu shi ne duk dan jarida da ba’a tantance shi ba tare da ba shi izinin shiga majalisar domin ya halarci zartarwa garkame shi za’ayi a waje har sai an kammala komi.

KU KARANTA:Fadan cikin gida na APC: Kalu ya nemi Buhari ya shiga tsakani

Sai dai kuma wata majiya mai karfi daga majalisar ta karyata wannan magana, inda take cigaba da tattaunawa da jagororin majalisar kan yadda za’ayi dan ‘yan jaridu a wannan rana.

Masu kula da yada labarai na majalisar na nan na tattaunawa da hukumar gudanarwa ta majalisar dokokin kan yadda wannan zabe da kuma bikin kaddamar da sabuwar majalisa zai kasance musamman duba ga bangaren manema labarai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel