Yanzu Yanzu: CCB ta saki sunayen sanatocin da za a bincika (jerin sunayen)

Yanzu Yanzu: CCB ta saki sunayen sanatocin da za a bincika (jerin sunayen)

Kwamitin Shugaban kasa na musamman da ke binciken dawo da dukiyar kasa (SPIP), a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, tace an tura lamarin rashawa da ya shafi yan siyasa takwas zuwa ga kotun kula da da’ar ma’aikata (CCB) don bincike.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa shugaban SPIP Okio ogbono-Obla yace kwamitin ta gano cewa yan siyasan sun mallaki kaddarori fiye da abunda suke samu da guminsu.

Obono-Obla ya bayyana cewa wadanda abun ya shafa sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark; Sanata Stella Oduah; SanataHope Uzodinma; Sanata Peter Nwaoboshi; Sanata Albert Bassey da kuma darekta ma’aikatar lantarki, ayyuka da muhalli, Ibrahim Musa Tumsah.

SPIP a baya ta shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Abuja akan yawancin wadanda sunayensu ya fada cikin jerin sunayen da aka tura ma CCB akan lamarin rashin bayyana kaddarorinsu.

Akwai kara akan Mark a babbar kotun tarayya, Abuja inda yake kalubalantan ayyukan kwamitin, musamman ikirarin kwamitin SPIP da ke cewa ya mallaki kaddarori a Abuja ta haramtacciyar hanya.

Karan da kwamitin ta shigar akan Sanata Oduah wanda aka tura ma Justis Ijeoma Ojukwu, amman babu matakin cigaba da kwamitin ta dauka tun daga lokacin da aka shigar da karan a shekaran da ya gabata.

Karan Uzosinma ya kasance a gaban Justis Okon Abang. Amman ofishin Atoni-Janar a tarayya a kwanan nan ta karbi karan daga SPIP don zartar da hukunci.

Karan Sanata Bassey na a gaban Justis John Tsoho.

Yawancin wadanda sunayensu ke a jerin kararrakin sunyi musun cewa kwamitin SPIP bata da karfin daukaka kara akan su, yayin da suke misali da hukuncin kotun daukaka kara a shari’ar Tumsah.

KU KARANTA KUMA: Ka tuna mulki na dan lokaci ne, mai karewa ne – Shehu Sani ya roki Ganduje

Kwamitin majalisa na musamman dake binciken halacci na kwamitin ta bayyana sanarwan a ranar Alhamis, 24 ga watan Afrilu, a lokacin sauraron karan.

Kwamitin, wanda Aliyu Ahman Pategi ke shugabanta yace kwamitin da Okio Obono-Obla ke jagoranta haramtacciya ce bisa dalilin karancin dokokin da ya kaddamar da ita, yanayin ayyukanta da ke kalubalantan hukumomin gwamnati kamar kotun kula da da’ar ma’aikata (CCB) wacce ke dauke da nauyin kwamitin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel