Ka tuna mulki na dan lokaci ne, mai karewa ne – Shehu Sani ya roki Ganduje

Ka tuna mulki na dan lokaci ne, mai karewa ne – Shehu Sani ya roki Ganduje

- Shehu Sani ya roki gwamnatin jihar Kano da ta tausasa zuciyarta akan Sarki Muhammadu Sanusi

- Sani na so Gwamna Abdullahi Ganduje ya san cewa mulki na dan lokaci ne kuma mai karewa ne

- Furucin Sanatan ya biyo bayan wata takardar neman ba’asi da aka aike wa sarki inda aka bukaci ya amsa ciki sa’o’i 24

Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Shehu Sani, ya roki gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje da ya tausasa matakan gwamnati akan Sarki Muhammadu Sanusi.

Sani ya bukaci gwamnan da ya gane cewa mulki na dan lokaci ne kuma yana karewa a karshe.

Gwamnatin jihar a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni ta aika takardar neman ba’asi ga sarki inda ta nemi ya amsa cikin sa’o’i 24.

Neman ba’asin na da alaka da zargin da hukumar yaki da rashawa na jihar Kano ke yi akan sarkin.

KU KARANTA KUMA: Majalisar dokoki ta tara: Na hango tarin bala’i da ke tunkarowa - Ndume

An tattaro cewa an ba sarki Sanusi sa’o’i 24 ya amsa tuhumar da ake masa a takardar wanda suka hada da zargin almubazaranci da kudade.

Da yake martani Sani yace: “Mulki na dan lokaci ne kuma mai karewa; ina rokon gwamnan Kano da ya sake duba sannan ya janye tsaurinsa akan Sarki Sanusi Lamido.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel