Mafi karancin albashi: Gwamnonin PDP sun shirya biyan N30,000

Mafi karancin albashi: Gwamnonin PDP sun shirya biyan N30,000

- Gwamnoni PDP sun jaddada shirinsu na biyan mafi karancin albashin N30,000 kamar yadda shugaban kasa ya kaddamar

- Shugaban gwamnonin PDP, Seriake Dickson ne ya bayyana wannan aniya tasu a Abuja bayan kungiyarsu ta kammala wata ganawa ta musamman

Gwamnonin jam’iyar PDP sun bayyana cewa a shirye suke tsaf domin biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kudurin ya zama doka a yanzu.

Shugaban gwamnonin PDP Seriake Dickson na Bayelsa ne yayi wannan furucin yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja jim kadan bayan kungiyarsu ta gwamnonin PDP ta kammala wata ganawa ta musamman a safiyar Juma’a.

Dickson ya ce, “a shirye muke da mu biya mafi karancin albashin a jihohinmu domin rage ma ma’aikata halin kuncin da suke ciki.”

Ya kuma roki shugaban kasa da yayi gaggawar mika kudurin zuwa ga majalisa mai shigowa domin a karasa kasafta yadda tsarin biyan mafi karancin albashin zai kasance, kana kuma a fara biyan ma’aikata nan take.

KU KARANTA:Dalilin janye takara ta, inji Goje

“ Kiris kawai muke jira mu gwamnonin PDP mu fara biyan mafi karancin albashin kamar yadda gwamnatin tarayya ta sanar kan N30,000.

“ Kokarin da muke a nan shine mu rage halin kunci da tabarbarewar tattalin arziki da ma’aikatan ke fama da shi tun zuwan gwamnatin APC. Dan abinda ake biyansu ba isar su yake ba.

“A don haka muke kira ga gwamnatin tarayya da tayi gaggawar kaddamar da wannan tsarin domin ganin a fara biyan ma’aikatan wannan kudi.” Inji gwamnan.

Dickson ya sake wanke kansu daga zargin cewa suna handame dukiyar kananan hukumomi inda yace, “ ina rokon gwamnatin tarayya da ta fadi sunayen jihohin dake aikata wannan rashin gaskiya, mu sam irin wannan dabi’a ba halinmu bane.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel