Majalisar dokoki ta tara: Na hango tarin bala’i da ke tunkarowa - Ndume

Majalisar dokoki ta tara: Na hango tarin bala’i da ke tunkarowa - Ndume

Tsohon shugaban masu rinjayi a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni ya bayyana cewa dole majalisar dattawa na tara tayi aiki don kare yancin ta don gujewa rigingimu a zaman majalisar.

Sanatan mai wakiltan Borno ta kudu ya bayyana cewa abu guda da ya kamata kowace majalisa ta kasance da shi ita ce yanci wacce zata yi iya kokarinta wajen kare wannan yancin.

Ndume wanda ya kasance daya daga yan takara dake kan gaba a wajen neman shugabancin majalisar dattawa yayi magana yayinda yake bada gudumuwar shi a taron bankwana na majalisar dattawa ta takwas.

Ya bayyana cewa banbancin dake tsakanin damukardiyya da kuma gwamnatin soja shine yancin majalisar dokoki.

Ya dage cewa dole a girmama majalisar a matsayin alamar damukardiyya wacce dole a kare yancinta a dukkan lokuta.

Ya bayyana cewa majalissan ta kasance ginshikin damukardiyya a kowace kasa.

KU KARANTA KUMA: Ban yi danasanin abunda na aikata ba a kan Zamfara – Marafa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Ali Ndume, ya ce ba zai janye takarar sa ba yayin babban zaben da za a gudanar a ranar 11 ga watan Yuni a zauren majalisar dake garin Abuja.

Ndume wanda ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Alhamis, ya ce ba ya bukatar kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wata ziyara domin sauya ra'ayin sa na janye takarar neman shugabancin sabuwar majalisar dattawan kasar nan.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Sanata Ndume ya ce ba ya da wata bukatar neman shawarar shugaban kasa Buhari domin yanye takara ga Sanata Ahmed Lawan wanda ya kasance daya daga cikin masu hankoron kujerar jagoranci a majalisar dattawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel