Fadan cikin gida na APC: Kalu ya nemi Buhari ya shiga tsakani

Fadan cikin gida na APC: Kalu ya nemi Buhari ya shiga tsakani

- Orji Kalu ya roki shugaban kasa yayi kokarin sasanta tsakanin Oyegun tsohon shugaban APC da kuma shugabanta na yanzu Adams Oshiomole

- Kalu yayi wannan kiran ne ranar Juma'a a jihar Legas yayin da yake zantawa da manema labarai

Tsohon gwamnan jihar Abia Dakta Orji Kalu ya nemi shugaba Buhari ya sanya baki cikin rikicin dake aukuwa a jam’iyar APC ta kasa tsakanin shugaban jam’iyar Adams Oshiomole da kuma wanda ya gabace shi kan kujerar John Odigie Oyegun.

Kalu yayi wannan kiran ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad dake Ikeja babban birnin jihar Legas.

Ya ce, “Akwai bukatar shugaban kasa ya shiga cikin lamarin domin dinke barakar da aka samu cikin jam’iyar a halin yanzu. Yin hakan shi kadai ne zai baiwa APC damar cika alkawurran da suka yiwa ‘yan Najeriya.

“Ko shakka babu wannan abin dake aukuwa tsakaninsu shi ake kira adon dimokuradiyya saboda dole ya kasance ana samun sabanin ra’ayi.

KU KARANTA:Dalilin janye takara ta, inji Goje

“A don haka muna kira ga shugaban kasa da ya sanya baki domin sasantawa tsakanin Oyegun da Oshiomole saboda cigaban jam’iyarmu ta APC. Ina da yakinin cewa shugaban kasa zai sasanta tsakaninsu kamar yadda yayiwa Lawan da Goje.

“A da can shugaban kasa bai son sanya kansa cikin irin wadannan lamuran amma yanzu ya fahimci muhimmancin yin hakan domin maslahar siyasar APC.” Inji Kalu.

Bugu da kari, Orji Kalu wanda shine zababben sanata mai wakiltar Abia ta Arewa ya sake jaddada kudurinsa na zama mataimakin shugaban sabuwar majalisa ta 9.

Kamar yadda yace, “ Ina nan kan bakata har ila yau, kuma na tsaya takarar nan ne da yakinin cewa zan yi nasara kuma zamu kawo canji ta hanyar hada hannu da majalisar zartarwa domin cika muradin yan kasa.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel