Muna nazari akan takardar da Ganduje ya aike mana – Shugaban ma’aikatan Sanusi

Muna nazari akan takardar da Ganduje ya aike mana – Shugaban ma’aikatan Sanusi

Munir Sanusi, Shugaban ma’aikatan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, yace masarautar na nazari akan irin abunda ke kunshe a takardar da aka aiko wa sarkin.

Ofishin sakataren gwamnatin jihar ta aike da takardar neman ba'asi kan tuhumar da ake yi wa sarkin na yin bushasha da makudan kudaden masarauta a madadin Gwamna Abdullahi Ganduje.

Wata majiya ta ruwaito cewa ana zargin masarautar da yin fakaca da kudade.

Shugaban ma’aikatan ya tabbatar da karban wasikar, cewa an bukaci sarki da ya bayar da amsa cikin sa’o’i 48.

“Mun karbi takardar neman ba'asi a yau (Alhamis). Gwamnatin ta nemi samun amsa cikin sa’o’i 48 daga mai martaba. Fada na nazari akan abunda takardar ya kunsa,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Ban yi danasanin abunda na aikata ba a kan Zamfara – Marafa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tataburza dake tsakanin gwamnatin jahar Kano da fadar masarautar Kano ta kara zafafa, inda a yanzu Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da tsare tsaren tsige mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II daga kujerar sarauta.

Majiyarmu ta ruwaito gwamnan ya aika ma Sarki wata takarda dake kunshe da dukkanin tuhume tuhumen da gwamnati ke masa dangane da almubazzarancin kudade, inda ya bukaci ya bashi amsa cikin sa’o’I 24.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel