Ban yi danasanin abunda na aikata ba a kan Zamfara – Marafa

Ban yi danasanin abunda na aikata ba a kan Zamfara – Marafa

- Sanata Kabiru Garba Marafa, ya bayyana cewa bai yi danasanin duk wani mataki da ya dauka na cewa lallai APC reshen jihar Zamfara bata gudanar da zaben fidda gwani ba

- Marafa yace mutanen Zamfara na farin ciki da hukuncin kotun koli da ya kori dukkanin zababben yan APC a jihar

- Yace koda dai bai so ace jam’iyyar adawa ta PDP ta amfana daga matakinsa ba, tuna ya amince da hukuncin

Sanata mai wakiltan yankin Zamfara ta tsakiya, Kabiru Garba Marafa, ya bayyana cewa bai yi danasanin duk wani mataki da ya dauka na cewa lallai APC reshen jihar Zamfara bata gudanar da zaben fidda gwani ba a watan Oktoban shekarar da ya gabata.

Marafa wanda karar da ya shigar kotu yayi sanadiyar soke dukkanin zaben fidda gwanin da jam’iyyar ta gudanar a jihar, yace mutanen Zamfara na farin ciki da hukuncin kotun koli da ya kori dukkanin zababben yan APC a jihar.

Da yake Magana a taron bankwana na majalisar dattawa na takwas a jiya Alhamis, 6 ga watan Yuni, Marafa yace koda dai bai so ace jam’iyyar adawa ta PDP ta amfana daga matakinsa ba, tuna ya amince da hukuncin.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin majalisa: Ya tabbata Lawan ko Ndume ne za su gaje ni – Saraki Read

“Ban yi danasani kan abunda nayi ba. An haife ni ne domin nayi yaki, kuma zan ci gaaba da yaki. Mutanen jihar Zamfara sun yi farin ciki da abunda ya faru,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel