Yan Boko Haram sun dandana kudarsu a hannun Sojojin Najeriya a Adamawa

Yan Boko Haram sun dandana kudarsu a hannun Sojojin Najeriya a Adamawa

Dakarun rundunar Sojin Najeriya sun dandana ma mayakan Boko Haram azaba a yayin da suka dakile wani hari da yan ta’addan suka yi yunkurin kaiwa a karamar hukumar Madagali na jahar Adamawa, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito anyi wannan arangama tsakanin Sojoji da yan ta’adda ne a ranar Talatar data gabata a kauyen Gulak, dake cikin karamar hukumar Madagali, inda Sojojin suka tare yan ta’addan bayan samun rahoton shirin kaddamar da harin.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta kaddamar da bincike akan mataimakin Oshiomole

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa Sojojin sun kwace manyan motocin yaki masu dauke da bindigu guda biyu, sa’annan sun kashe da dama, tare da jikkata wasu da dama daga cikinsu.

Wani mazaunin garin mai suna Salihu Salimu ya bayyana cewa “A yanzu kam Sojoji suna kokari matuka, inda suke farautar yan ta’addan ruwa a jallo, sun daina tsayawa jiran yan ta’addan su kai hari kafin su far musu, wannan shine batun da jama’a ke tattaunawa a yanzu.”

Shima tsohon shugaban karamar hukumar Madagali, Muhammad Yusuf ya jinjina ma jarumtar da Sojojin Najeriya suke nunawa a yakin da suke yi da yan ta’adda, inda yayi kira ga gwamnati ta kara tura musu Sojoji a yankin.

“Yawancin kauyukanmu babu kowa a cikinsu, sun zama kufai saboda yawaitan hare hare, amma irin wannan nasarar da Sojojinmu suka samu yana bamu kwarin gwiwa, kuma yana kara mana yakinin samun nasara, sa’annan gwamnanmu yayi alkawarin baiwa jami’an tsaro goyon baya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel