Kaakakin majalisa, Dasuki da yaron Bafarawa sun zama kwamishinoni a gwamnatin Tambuwal

Kaakakin majalisa, Dasuki da yaron Bafarawa sun zama kwamishinoni a gwamnatin Tambuwal

Gwamnan jahar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya nada yaron tsohon gwamnan jahar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, yaron tsohon Sarkin Musulmi, Sultan Maccido, Abdulsamad Dasuki a matsayin sabbin kwamishinoni.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni ne majalisar dokokin jahar Sakkwato ne ta kammala tantance sunayen da gwamnan ya turo mata, tare da amincewa dasu a matsayin wadanda suka cancanci a nadasu kwamishinoni.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta kaddamar da bincike akan mataimakin Oshiomole

Mataimakin kaakakin majalisar dokokin jahar, Abubakar Magaji ne ya jagoranci zaman majalisar, inda yace majalisar ta amince da sunayen sabbin kwamishinonin ba tare da wani dogon bincike ba saboda nagartarsu.

Daga cikin wadanda majalisar ta amince da sunayensu akwai kaakakin majalisar dokokin jahar mai barin gado, Salihu Maidaji, babban yaron tsohon gwamna Attahiru Bafarawa, Sagir da kuma yaron tsohon sarkin Musulmi, kuma dan majalisar tarayya mai garin gado, Abdussamad Dasuki.

Sauran sun hada da tsohon sakataren gwamnatin jahar, Farfesa Bashir Garba, tsofaffin yan majalisun tarayya, Umar Bature da Arzika Tureta, dan majalisar dokokin jahar daga jam’iyyar PDP Balarabe Kakakale.

Har ila yau daga cikin sunayen da majalisar ta amince da nadasu mukamin kwamishina a jahar Sakkwato akwai tsohon hafsan Soja, kanal Garba Moyi, Abdullahi Maigwandu, babban lauya Sulaiman Usman SAN, Kulu Haruna da kuma Farfesa Aisha Madawaki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel