Jam’iyyar APC ta kaddamar da bincike akan mataimakin Oshiomole

Jam’iyyar APC ta kaddamar da bincike akan mataimakin Oshiomole

Uwar jam’iyyar APC ta kasa ta kafa wata kwamitin mutane biyar da zata gudanar da bincike akan mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen yankin Arewacin Najeriya, Sanata Lawal Shuaibu da nufin ladabtar dashi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni inda yace jam’iyyar ta dauki wannan mataki ne a zamanta na 38 daya gudana a sakatariyarta dake Abuja.

KU KARANTA: Duniya mai yayi: Sabon gwamnan jahar Imo ya fara binciken Rochas Okorocha

Jam’iyyar APC ta kaddamar da bincike akan mataimakin Oshiomole

Lawan
Source: Twitter

A kwanakin baya ne Lawan Shuaibu ya aika ma shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole takarda inda ya nemi yayi murabus daga kujerar shugabancin jam’iyyar saboda a cewarsa baya tsinana ma jam’iyyar amfanin komai, kuma bai iya tafiyar da jam’iyyar ba.

Sai dai kaakakin jam’iyyar, Issa-Onilu ya bayyana cewa duk da kiraye kirayen tsige Oshiomole da Lawan yayi, amma shuwagabannin jam’iyyar APC na jahohin Najeriya 36 sun jaddada goyon bayansa ga shugaba Oshiomole.

“A zaman uwar jam’iyyar APC na 38 daya gudana a ranar 27, 28 da 6 ga watan Yuni, APC ta tattauna batutuwa da dama, daga ciki harda halin da jam’iyyar ke ciki, bayan doguwar tattauna jam’iyyar ta amince da shugabancin Oshiomole.

“Sa’annan ta kafa kwamitin mutane biyar a karkashin jagoranci Otunba Niyi Adebayo domin su binciki Lawan game da zarge zargen da yayi ma shugaban jam’iyyar Oshiomole, da kuma zargin ingiza Sanatoci da yan majalisun dokoki domin su tsige shugaban jam’iyyar.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin APC yace uwar jam’iyyar ta bukaci kwamitin ta dawo mata da rahoton binciken data gudanar bayan kwanaki bakwai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel