Duniya mai yayi: Sabon gwamnan jahar Imo ya fara binciken Rochas Okorocha

Duniya mai yayi: Sabon gwamnan jahar Imo ya fara binciken Rochas Okorocha

Sabon gwamnan jahar Imo, Emeka Ihedioha ya kafa kwamitin mutane 8 domin kaddamar da bincike akan yadda tsohon gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha ya kashe kudaden jahar a zamanin mulkinsa daga 2011 zuwa 2019.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gwamna Emeka ya nada Dakta Abraham Nwanmkwo ne a matsayin shugaban wannan kwamiti da zata bi diddigin yadda tsohon gwamnan ya kashe kudaden da suka shigo ma jahar a iya wa’adin mulkinsa.

KU KARANTA: Tsiyar yan NEPA: Mutane 350,000 zasu koma rayuwa a cikin duhu a jahar Kano

A jawabin gwamnan ta bakin sakataren watsa labarunsa, Mista Chibuike Onyeukwu wanda yace babban aikin da ake bukatar kwamitin ta gudanar shine tabbatar da duk bankunan da kudaden gwamnatin jahar suke, nawa ne kudaden da kuma rubuta rahoto akan hakan.

“Haka zalika kwamitin zata bi diddigin inda aka samo kudaden da gwamnatin ta kashe wajen gudanar da duk ayyukan da ta gudanar, bin diddigin adadin kudin ruwan daya karu akan kudaden gwamnati dake bankuna, da kuma bashin da ake bin jahar.

“Bin diddigin yadda aka raba ma ma’aikatu da hukumomin gwamnati kudade daga shekarar 2011-2019, da kuma yadda suka kashesu, bin bahasin aikin hukumar tattara kudaden haraji na jahar Imo tare da lalubo hanyoyin ingantata.” Inji shi.

A wani labarin kuma, a fitarsa na farko daga fadar gwamnati, sabon gwamnan ya kai ziyara zuwa ga al’ummar Musulmai mazauna garin Owerri domin tayasu murnar zagayowar ranar karamar Sallah.

Gwamnan a jawabinsa ya bayyana cewa zai basu gudunmuwar da suke bukata domin kawo cigaba a unguwar Hausawa, tare da alkawarin samar da hanyoyin wucewar ruwa, da kuma kammala ginin sabon fadar Sarkin Hausawan jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel