Shuwagabannin APC sun jaddada goyon bayansu ga Adams Oshiomole

Shuwagabannin APC sun jaddada goyon bayansu ga Adams Oshiomole

Shuwagabannin jam’iyyar APC na rassan jahohin Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga shugaban jam’iyyar ta kasa, Kwamared Adams Oshiomole, inda suka ce shine wanda yafi cancanta ya jagoranci jam’iyyar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sakataren kungiyar shuwagabannin jam’iyyar APC, kuma shugaban APC reshen jahar Enugu, Ben Nwoye ne ya bayyana haka a madadin sauran takwarorinsa yayin da yake ganawa da manema labaru a sakatariyan jam’iyyar.

KU KARANTA: Tsiyar yan NEPA: Mutane 350,000 zasu koma rayuwa a cikin duhu a jahar Kano

Shuwagabannin APC sun jaddada goyon bayansu ga Adams Oshiomole

Shuwagabannin APC sun jaddada goyon bayansu ga Adams Oshiomole
Source: Twitter

Nwoye ya bayyana cewa duk da munanan rahotannin da ake watsawa game da shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole, su sun amince shine wanda yafi dacewa ya cigaba da rike jam’iyyar a wannan lokaci.

“Mun gana da shugaban jam’iyyarmu, da kuma sauran shuwagabannin jam’iyyar inda muka tattauna muhimman batutuwa, mun tabo batun hadin kan jam’iyyar, kuma daga karshen zaman mun jaddada goyon bayanmu ga shugaban APC Adams Oshiomole.” Inji shi.

Nwoye ya kara da cewa batancin da ake watsawa a kafafen sadarwa akan Adams Oshiomole ba wani bane illa kokarin yin batanci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma jam’iyyar APC gaba daya.

Daga karshe Nwoye yace Oshiomole nada karfin da zai iya tafiyar da jam’iyyar APC a wannan lokaci data kafa sabuwar gwamnati domin ciyar da Najeriya gaba.

Idan za’a tuna a ranar 28 ga watan Mayu ne mataimakin shugaban APC reshen Arewacin Najeriya, Sanata Lawal Shuaibu yayi kira ga shugaba Oshiomole da yayi murabus daga kujerarsa saboda ya kasa tsinana na APC komai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel