'Yan arewa na da damar fitowa takarar shugaban kasa a 2023 - Shittu

'Yan arewa na da damar fitowa takarar shugaban kasa a 2023 - Shittu

Tsohon Ministan Sadarwa, Mista Adebayo Shittu ya bayyana cewa yankin arewa na da dama fito da dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023, mutukar yana da cancantar da ake bukatar kowanne shugaban kasa ya samu

Jiya Alhamis ne tsohon Ministan Sadarwa na kasa, Mista Adebayo Shittu, ya bayyana cewa arewa na da damar da zata iya fito da dan takarar shugaban kasa a 2023, mutukar sun gabatar da wanda ya cancanta.

A lokacin da yake magana da manema labarai a Abuja, Shittu, wanda yake na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shi bai taba nuna bangaranci ba a siyasar sa, amma kullum abinda yake so shine yaga ya goyawa mutum na gari baya.

'Yan arewa na da damar fitowa takarar shugaban kasa a 2023 - Shittu

'Yan arewa na da damar fitowa takarar shugaban kasa a 2023 - Shittu
Source: Facebook

Ya ce: "Shi yadda ya sani shine, idan har zancen siyasa ake yi, to dole kowacce jam'iyya ta gabatar da zaben fidda gwani, kuma wanda ya samu nasara shine zai fito a matsayin dan takara.

"Dokar kasa bata ce dole sai dan yanki kaza ne zai fito takarar shugaban kasa ba. Abinda dokar kasa tace shine, duk inda shugaban kasa ya fito to mataimakinsa dolene ya fito daga wani yanki daban. Saboda haka siyasar kasar nan babu bangaranci a cikinta. Bamu zabi shugaba Buhari ba saboda ya fito daga yankin arewa, mun zabe shi ne saboda cancantar sa."

KU KARANTA: Dokar hana acaba: Sojoji sun kashe mutane 4 yayin da suke gabatar da zanga-zanga a jihar Adamawa

"Haka kuma Shittu ya kara dakko maganar rikicin shugabancin jam'iyyar APC, inda yake ganin laifin shugaban jam'iyyar na kasa, Comrade Adams Oshiomhole akan ruguza jam'iyyar ta APC."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel