Dokar hana acaba: Sojoji sun kashe mutane 4 yayin da suke gabatar da zanga-zanga a jihar Adamawa

Dokar hana acaba: Sojoji sun kashe mutane 4 yayin da suke gabatar da zanga-zanga a jihar Adamawa

- Sojoji sun kashe mutane hudu a jihar Adamawa lokacin da suke gabatar da zanga-zanga akan hana acaba

- Mutanen sun fito zanga-zangar ne saboda suna ganin babu wani dalili da zai saka gwamnati hana su hawa babur

Zanga-zanga akan hana acaba a garin Gurin dake karamar hukumar Fufore na jihar Adamawa, tayi sanadiyyar asarar rayukan mutum hudu a jiya.

Rahotanni sun nuna mutanen garin wanda ke da iyaka da kasar Kamaru sun fito da safiyar ranar Alhamis, inda suke zanga-zanga akan hana yin acaba a garin wanda hukumar 'yan sandan jihar ta sanya dokar watan da ya gabata.

Dokar hana acaba: Sojoji sun kashe mutane 4 yayin da suke gabatar da zanga-zanga a jihar Adamawa

Dokar hana acaba: Sojoji sun kashe mutane 4 yayin da suke gabatar da zanga-zanga a jihar Adamawa
Source: Facebook

Hukumar 'yan sandan tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar sun hana yin acaba a garin, inda suka yi bayanin cewa 'yan ta'adda suna amfani da babur ne gabatar da ta'addancin su.

Wani mutumi mazaunin garin wanda yayi magana da jaridar Vanguard, ya bayyana cewa sojoji sun harbi mutum biyu daga cikin masu zanga-zangar, inda suka mutu a take a gurin, inda wasu mutane biyu kuma suka mutu a hanyar zuwa kai su asibiti.

KU KARANTA: Saurayin da ya kone dangin budurwarsa zai fuskanci hukuncin kisa - Hukumar 'yan sanda

"Kwarai da gaske mutum hudu sun mutu sakamakon harbinsu da sojoji suka yi," in ji mutumin, inda ya kara da cewa mutanen sun yanke hukuncin fitowa zanga-zangar ne saboda basu ga wani dalili da zai saka a hanasu yin acaba a yankin nasu ba.

"Mutanen garin nan yawancin su manoma ne, suna bukatar babur domin zuwa gonakinsu, babur ne kawai hanyar tafiye-tafiye a garin," in ji mutumin.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar zanga-zangar, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar ya tura rundunar 'yan sanda garin, inda har yanzu basu kawo masa rahoton ko mutane sun mutu a garin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel