Gwamnonin PDP sun shiga taron sirri a Abuja

Gwamnonin PDP sun shiga taron sirri a Abuja

Zababun gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun shiga taron sirri a babban birnin tarayya, Abuja.

Wata majiya daga masaukin gwamnan Jihar Bayelsa ta ce babu alamar za a kammala taron nan kusa duk da cewa an kwashe sa'o'i hudu a wurin taron kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tsaffi da sabbin gwamnonin PDP karkashin jagorancin gwamnan jihar Bayelsa kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Seriake Dickson tare da Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Bukola Saraki sun hallarci taron.

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: NBC ta dakatar da AIT da Ray Power

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnonin suna tattauna lamuran kasa ne da kuma yadda jam'iyyar za ta kwato nasarar da ta ke ganin ta samu a zaben shugaban kasa na watan Fabrairun wannan shekarar.

Har wa yau, mahallarta taron kuma su na tattaunawa kan hanyoyin da za su bi wurin kallubalantar sakamakon zabukkan gwamnonin wasu jihohi da suke ganin anyi musu ba dai-dai ba da ma wasu muhimman batutuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel