Fashewar bam ta yi sanadin mutuwar mutane uku a kudancin Najeriya

Fashewar bam ta yi sanadin mutuwar mutane uku a kudancin Najeriya

Rundunar 'Yan sandan Najeriya reshen Jihar Imo, a ranar Alhamis 6 ga watan Yuni ta tabbatar da fashewar bam a garin Eziorsu da ke karamar hukumar Oguta na jihar da ya yi sanadiyar rasuwar mutane uku.

Vanguard ta ruwaito cewa kakakin rundunar 'yan sandan Jihar, Orlando Ikeokwu ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Rahoton ya ce Ikeokwu ya bayar da sunayen wadanda suka rasu kamar haka; Elvis Ukado; Kasiemobi Uzoma da Justice Adie.

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: An kama shugaban CAF, Ahmad Ahmad

"Wata bam ce da ba ta fashe ba a bola.

"Daya daga cikin wanda lamarin ya ritsa da su yana bugun karfen domin ya tankwara shi kwatsam sai bam din ya fashe ya kashe su uku nan take," inji shi.

Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Rabiu Ladodo da tawagarsa sun ziyarci inda bam din ya fashe a Oguta.

"Kwamishinan 'yan sandan yana son amfani da wannan damar ya gargadi mutane su rika sanar da hukuma duk lokacin da suka gano wani karfe da ake zargi bam ne saboda a gudanar da bincike kuma a kawar da shi idan akwai bukatar hakan," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel