Mambobi 60 na jam'iyyun adawa sun goyi bayan tikitin Gbajabiamila da Wase

Mambobi 60 na jam'iyyun adawa sun goyi bayan tikitin Gbajabiamila da Wase

Takarar Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban majalisar wakilai da honarabul Ahmed Idris Wase a matsayin mataimakinsa ta samu karin karfi bayan wata kungiyar sabbi da tsofin mambobin majalisar wakilai daga jam'iyyun adawa sun goya musu baya.

A cewar kungiyar, wacce honarabul Oluwole Oke (mamba a majalisar daga jihar Osun) ya ce kungiyar su ta mambobin majalisar ne da aka zaba a kananan jam'iyyun adawa daga sassan kasar nan. Ya kara da cewa kungiyarsu ta kunshi mambobi maza da mata.

A jawabin da kungiyar a ranar Alhamis, ta bayyana cewar ta yanke shawarar goyon bayan Gbajabiamila da Wase ne saboda wasu dalilai kamar haka:

"Na farko, a duk siyasar duniya mai hankali, duk lokacin da aka samu gibi a shugabancin majalisa, shugaban masu rinjaye a majalisa ne zai zama shugaban majalisar ba tare da wani wani abu ya yi masa waigi ba. Za a iya ganin misali a kan shugaban majalisa Nancy Pelosi.

Mambobi 60 na jam'iyyun adawa sun goyi bayan tikitin Gbajabiamila da Wase

Femi Gbajabiamila
Source: Twitter

"Na biyu, shugaban kasa, wanda ya fito daga jam'iyya daya da Gbajabiamila, ya zabe shi a matsayin dan takarar da yake so a zaba a kujerar shugabancin majalisar wakilai.

"Zaben Gbajabiamila zai kawo fahimtar juna a tsakanin bangaren majalisa da bangaren zartar wa a sabuwar gwmnatin da aka shiga.

DUBA WANNAN: Majalisar dattijai: Ndume ya yi magana a kan janyewar Goje

"Dalili na uku, Gbajabiamila gogagge ne a majalisa. Tun shekarar 2003 yake majalisa kuma ya nuna kansa a matsayin mai basira da kishin kasa, a saboda haka bamu ga wani dan takara da ya kai shi cancanta ba," a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa ta na mambobi 60 a majalisar wakilai tare da yin gare su da su goyi bayan tikitin Gbajabiamila da Wase a zaben shugabancin majalisar da za a yi a cikin sati mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel