Kalli bidiyon wasu fastoci 2 da suka musulunta cikin watan Ramadan

Kalli bidiyon wasu fastoci 2 da suka musulunta cikin watan Ramadan

Masu bibiyar kafafen sada zumunta suna da bayyana ra'ayoyin su kan wani faifan bidiyo da ke yaduwa inda aka nuna wasu fastoci biyu suna karbar shahada a yayin wani wa'azi da aka gudanar cikin watan Ramadan a Jihar Ogun.

Mutane kan sauya addinai domin neman kwanciyar hankali da dacewa a gobe kiyama sai dai ba kasafai ake samun labarin shugabanin ko malaman addini suna canja addini ba.

A halin yanzu dai bidiyon da ke nuna fastocin biyu na karbar shahada na musulunci yana da bazuwa a dandalin sada zumunta.

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: An kama shugaban CAF, Ahmad Ahmad

A cikin bidiyon, mutanen biyu sun karba shahada yayin wani wa'azin watan Ramadan da aka gudanar a Ilaro a jihar Ogun. Sun sauya sunayensu zuwa Muhammad Saheed da Mohammed Jami'u.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel