Bukola Saraki kaman Abacha ya ke - Sanatan PDP

Bukola Saraki kaman Abacha ya ke - Sanatan PDP

Obinna Ogba, Sanatan Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga Jihar Ebonyi ya kamanta Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki da tsohon shugaban mulkin soji na kasar, Janar Sani Abacha.

Abacha ya mulki Najeriya daga shekarar 1993 zuwa 1998.

Mutane da dama suna kyamar irin salon mulkinsa amma Ogba ya ce tsohon Janar din "mutumin kirki ne".

Ya ce lamarin tsaro bai tabarbare a zamanin Abacha kamar yadda ya ke ba a yanzu kuma ya kara da cewa tsohon shugaban mulkin sojin bai da masaniya kan wasu munanan abubuwa da aka aikata a zamanin mulkinsa.

DUBA WANNAN: Dan Najeriya ya yi rabon kayan tallafi ga al'umma a masallacin Makkah

Ogba ya yi wannan furucin ne yayin zaman majalisa na bankwana da aka gudanar a ranar Alhamis.

"Ina ganin mulkin Saraki ya yi kama da na Abacha. Ba shi da banbanci da Abacha. Ina daya daga cikin wadanda su kayi imanin cewa ba mu ta ba samun shugaba kamar Abacha ba. Zai yiwu ka so shi ko kuma ka ki shi," inji shi.

"Abacha mutumin kirki ne duk da irin abubuwan da mutane ke fadi a game da shi. Mutanen da ke zaginsa sun aikata abubuwan da suka fi nasa muni a yau. Lokacin Abacha bamu da matsalar tsaro kamar yadda muke da shi a yau. Mutumin ya aikata abubuwan alheri masu yawa.

"Duk inda ya ke, Allah zai cigaba da saka masa da alheri. Shi ne ya bamu Jihar Ebonyi. Allah zai cigaba da saka masa da alheri da kai ma (Saraki)."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel