Ndume ya yi magana a kan janyewar Goje daga takarar kujerar shugabancin majalisar dattijai

Ndume ya yi magana a kan janyewar Goje daga takarar kujerar shugabancin majalisar dattijai

Sanatan jihar Borno a majalisar dattijai, Ali Ndume, ya ce har yanzu yana takarar kujerar shugabancin majalisar dattijai.

Ndume ya yi wannan kalami ne sa'o'i kadan bayan Danjuma Goje, mai takarar neman kujerar shugabancin majalisar, ya janye takarar sa tare da bayyana goyon bayansa ga takarar Ahmed Lawan.

A ranar Alhamis ne Goje ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga takarar Lawan bayan wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa, Villa, da ke Abuja, birnin tarayya.

Ya bayyana cewar ya janye takararsa ne saboda shugaba Buhari ya bukaci ya yi hakan. Ya kara da cewa ya janye domin mutunta zabin jam'iyya da kuma inganta hadin kai a cikin jam'iyyar.

Jam'iyyar APC ta dade da bayyana cewar Lawan ne dan takarar da take so a zaba a matsayin shugaban majalisar dattijai.

Ndume ya yi magana a kan janyewar Goje daga takarar kujerar shugabancin majalisar dattijai

Sanata Ali Ndume
Source: Facebook

Sai dai, Ndume ya bayyana cewar jam'iyyar APC ta yi gaban kanta ne kawai wajen zabar Lawan ba tare da tunanin ko daukacin shugabancin jam'iyya na tare da shi ba.

Tuni shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, da jagoranta na kasa, Bola Tinubu, suka yi kira ga Ndume da ragowar fusatattun mambobin jam'iyyar APC da su goyi bayan takarar Lawan ko kuma su tattara kayansu su bar jam'iyyar idan ba zasu yi biyayya ga umarnin jam'iyyar ba.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta kwace rijiyoyin man fetur 6

A jawabin da ya fitar a ranar Alhamis, Ndume ya ce ya yi farinciki da janyewar Goje tare da bayyana cewar hakan ya rage yawan masu neman kujerar shugabancin majalisar dattijai zuwa mutum biyu kacal.

"Ina mai tabbatar wa da jama'a cewa har yanzu ina takarar neman kujerar shugabacin majalisar dattijai. Da Allah na dogara domin shine ke bayar da mulki, a saboda haka bani da wata damuwa.

"Na yi maraba da janyewar Goje, hakan ya rage mu biyu kawai da ragowar sanatoci zasu zabi wanda suke so ya jagorance su domin kawowa kasa cigaba," a cewar Ndume.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel