Saraki ya bayyana ranar da tafi bakanta masa rai a majalisa

Saraki ya bayyana ranar da tafi bakanta masa rai a majalisa

Shugaban majalisar dattawar Najeriya, Dakta Bukola Saraki ya ce ranar 18 ga watan Afrilun 2018 ce ranar da tafi bakanta masa rai a tsawon mulkinsa.

Ya ce a ranar ne aka yi kuste cikin majalisar aka sace sandan ikon majalisar.

Saraki ya yi wannan furucin ne a ranar Alhamis yayin da ya ke jawabinsa na bankwana wadda shine zama na karshe da majalisar karo na 8 za ta yi.

Kafin karanto jawabinsa na bankwana, Saraki ya bukaci takwarorinsa a majalisa su saurara na minti daya domin karrama takwarorinsu uku da suka rasu wato Ali Wakili (Bauchi ta Kudu), Isiaka Adeleke (Osun ta Yamma) da Bukar Mustapha (Katsina ta Arewa).

DUBA WANNAN: Dan Najeriya ya yi rabon kayan tallafi ga al'umma a masallacin Makkah

Saraki ya mika godiyarsa ga takwarorinsa bisa goyon baya ta suka bashi har a lokutan da suke fuskantar kallubale.

"Kutsen da wasu jami'an tsaro masu dauke da makamai su ka yi a majalisa a watan Augustan 2018 ranar ce ta bakin ciki. Wannan ranar ce ta fi bakanta min rai a majalisa duk da cewa hakan ya bawa majalisa damar cin gashin kanta da kuma nasarar demokradiyya.

"Ta kuma kasance ranar nuna alaka ta musamman da ke tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai ta yadda suka hada kai wuri guda domin kushe wadanda su kayi kutsen. Ina godiya da mambobin majalisar wakilai ta 8 domin hadin kan da suka bamu ne ya sa mu kayi nasara."

Saraki ya kuma yi alfahari da dattaku da takwarorinsa suka nuna inda ya ce ba a samu wani babban abin kunya ba cikin shekaru hudu na majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel