Makiyaya ba su da dalilin kai hari yankin Kudu maso Gabashin Najeriya - Miyetti Allah

Makiyaya ba su da dalilin kai hari yankin Kudu maso Gabashin Najeriya - Miyetti Allah

Mun samu rahoton cewa kungiyar makiyayan Fulani ta Najeriya Miyetti Allah reshen Kudu maso Gabashin kasar nan, ta ce ba wani takun saka ko kuma gaba a tsakanin ta da kowace jiha a yankin ballantana ta kai ga kulla aniyyar kai mata hari.

Kungiyar cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a birnin Awka na jihar Anambra, ta musanta jita jitar kafofin watsa labarai dake yada rahoton cewa ta yi ikirarin makiyaya za su tayar da tsaye a yankin a sakamakon haramta masu wuraren kiwo.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen Kudu maso Gabashin kasar nan, Alhaji Gidado Sidikki, shi ne ya bayar da shaidar hakan tare da bayyana takaicin sa dangane da yaduwar wannan kanzon kurege.

Yayin barrantar da kungiyar Miyetti Allah daga wannan munanan kalamai, Alhaji Sidikki ya nemi daukacin al'ummar kasar nan da su dawo daga rakiyar rade-radin da ke yaduwa domin cimma wata manufa da ba za ta haifar da zaman lafiya ba a kasar nan.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa: Ba zan janye takara ta ba - Ndume

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa Alhaji Sidikki ya kuma yaba da kyakkyawar alakar dake tsakanin 'ya'yan kungiyar na makiyaya da kuma daukacin al'ummar yankin Kudu maso Gabas tare da jagororin su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel