Shugabancin majalisa: Ya tabbata Lawan ko Ndume ne za su gaje ni – Saraki

Shugabancin majalisa: Ya tabbata Lawan ko Ndume ne za su gaje ni – Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya bayyana cewa yanzu a bayyane yake cewa imma Sanata Ali Ndume mai wakiltan Borno ta kudu ko kuma Ahmed Lawan Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan ne za su gaje shi a wajen shugabancin majalisar.

Saraki yayi magana ne a taron bankwana na majalisar dattawa na takwas wanda aka gudanar a yau Alhamis, 6 ga watan Yuni.

Shugaban majalisar wanda ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da majalisar ta samu ya mika godiya da jinjina ga sanatocin akan irin goyon bayan da suka bashi a lokacin da ya shugabance su.

“Ina mika godiya ga Shugaban masu rinjaye a majalisa Ahmad Lawan, ka taka rawar ganinka anan kuma tarihi ya tabbatar da hakan. Sannan ina mika godiya ga tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisa Ali Ndume, kaima ka bayar da naka gudunmawar. Tsakanin tsohon Shugaban masu rinjaye da maai ci a yanzu, a bayyane yake cewa daya daga cikinku zai zama Shugaban majalisar dattawa.

“Duk wanda yayi nasara, ina yi masa fatan alkhairi. Abunda nasani: a kowani yanayi, mu yi iya bakin kokarinmu wajen ganin ra’ayin al’umma ne kan gaba. Mu sanya a ranmu cewa mulki abune mai shudewa."

KU KARANTA KUMA: Komai yayi farko zai yi karshe: An ba Sanatoci kwana 3 su mika makulan ofishinsu

Lawan dai shine zabin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) amma Ali Ndume ya ki janyewa daga tseren.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel