Majalisar Dattawa: Ba zan janye takara ta ba - Ndume

Majalisar Dattawa: Ba zan janye takara ta ba - Ndume

Daya daga cikin manyan masu hankoron kujerar shugabancin majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ce ba zai janye takarar sa ba yayin babban zaben da za a gudanar a ranar 11 ga watan Yuni a zauren majalisar dake garin Abuja.

Ndume wanda ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Alhamis, ya ce ba ya bukatar kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wata ziyara domin sauya ra'ayin sa na janye takarar neman shugabancin sabuwar majalisar dattawan kasar nan.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Sanata Ndume ya ce ba ya da wata bukatar neman shawarar shugaban kasa Buhari domin yanye takara ga Sanata Ahmed Lawan wanda ya kasance daya daga cikin masu hankoron kujerar jagoranci a majalisar dattawa.

Tsohon shugaba a majalisar dattawan kasar nan ya musanta rahoton dake yaduwa a dandalan sada zumunta na cewar shugaban kasa Buhari ya gayyace shi zuwa fadar Villa domin umurtar sa akan janye takara.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Gwamna Zulum ya kara wa dakarun sa kai alawus a jihar Borno

Cikin yakini na neman yardar Mai Duka gami da kyautata zato, Sanata Ndume ya ce yana nan akan bakan sa ta yin takarar shugabancin sabuwar majalisar dattawan kasar nan da za a gudanar a ranar Talata ta mako mai zuwa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a yau Alhamis, 6 ga watan Yuni, Sanata Danjuma Goje, ya janye wa Sanata Ahmad Lawan takarar sa ta neman jagorancin sabuwar majalisar dattawa bayan ganawa da shugaban kasa Buhari a fadar Villa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel