Yanzu Yanzu: Za mu ba gwamnatin PDP mai mulki a Zamfara adawa mai inganci - APC

Yanzu Yanzu: Za mu ba gwamnatin PDP mai mulki a Zamfara adawa mai inganci - APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Zamfara tayi alkawarin samar da adawa mai inganci ga jam’iyya mai mulki ta Peoples Democratic Party (PDP) a jihar.

Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Lawal Liman ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga manema labarai a Gusau a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni, cewa mambobin jam’iyyarsa za su ci gaba da kasancewa masu bin doka, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.

“Mun yarda cewa nasarar PDP a jihar nufi ne na Allah sannan mun amince da hakan da zuciya daya, damuwarmu shine yanda jihar za ta ci gaba” inji shi.

Ya nuna bakin ciki cewa wasu mutane da ba a san ko su wanene ba na bata allunan APC a fadin jihar.

Don haka yayi kira ga gwamnatin jihar da kuna shugabancin PDP da su wayar da kan magoya bayansu akan munanan halayya.

KU KARANTA KUMA: Jagorancin majalisa: PDP ta karyata cewa tayi mubaya’a ga wasu yan takara

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Zamfara, Dr. Bello Muhammad Mutawalle, ya amince da dakatar da Sarkin Maru, Alhaji Abubakar Chika Ibrahim, da hakimin garin Kanoma, Alhaji Ahmad Lawal, ba tare da bata lokaci ba.

A wani jawabi dauke da sa hannun darakta janar na harkokin labaran gidan gwamnati, Alhaji Yusuf Idris, a dakatar da shugabannin biyu ne biyo bayan yawan korafe-korafe game da su akan zargin cewa suna da hannu a lamarin ta’addanci da fashi da makami.

Yace za a ci gaba da dakatar da sarkin da hakimin har sai anji sakamakon binciken farko daga kwamitin bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel