An tafka babban rashi: Buhari ya taya Sulu Gambari alhinin mutuwar mahaifiyarsa

An tafka babban rashi: Buhari ya taya Sulu Gambari alhinin mutuwar mahaifiyarsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya mai martaba sarkin Ilorin da kafatanin al’ummar masarautar alhinin mutuwar Alhaja Aishat Nma Sulukarnaini-Gambari, mahaifiyar Sarki Alhaji Ibrahim Sulu Gambari.

Buhari ya bayyana wannan alhini ne ta bakin kaakakinsa, Malam Garba Shehu, a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni a babban birnin tarayya Abuja, inda yayi ma Sarkin da iyalansa ta’aziyyar mutuwar Alhaja Aishat Nma Sulukarnaini-Gambari.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Ganduje ya fara shirin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II

An tafka babban rashi: Buhari ya taya Sulu Gambari alhinin mutuwar mahaifiyarsa

Marigayiya Aisha
Source: Facebook

Haka zalika Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin jahar Kwara kwata game da wannan babban rashi da jahar ta tafka, inda yace kyawawan halayen marigayiya Alhaja Aishat Nma Sulukarnaini-Gambari sun ketare fada, har sun tsallaka ga talakawan masarautar.

Daga nan Buhari ya kara da cewa tabbas za’ayi rashin Alhaja Aishat Nma Sulukarnaini-Gambari, kuma za’a dinga tunata da kyawawan halayenta da suka hada da tsoron Allah, saukin kai da kuma taimaka ma gajiyayyu.

Idan za’a tuna Legit.ng ta ruwaito muku cewa mahaifiyar Sarkin ta rasu tana da shekaru 124 a duniya, kuma jigo ce a masarautar Illori gaba da baya saboda kasancewarta

- Jika ga Sarkin Illori na 7

- Diya ga Sarkin Illori na 8

- Matar Sarkin Illori na 9

- Kanwar Sarkin Illori na 10

- Mahaifiyar Sarkin Illori na 11

Daga karshe shugaban kasa Buhari yayi addu’ar Allah Ya yi mata rahama, ya saka mata da gidan Alhannar Firdausi, sa’annan ya kara addu’ar Allah ya baiwa iyalanta, yan uwa da abokan arziki hakurin rashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel