Da dumi dumi: Ganduje ya fara shirin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II

Da dumi dumi: Ganduje ya fara shirin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II

Tataburza dake tsakanin gwamnatin jahar Kano da fadar masarautar Kano ta kara zafafa, inda a yanzu Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da tsare tsaren tsige mai martaba Sarki Muhammadu Sunusi II daga kujerar sarauta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya aika ma Sarki wata takarda dake kunshe da dukkanin tuhume tuhumen da gwamnati ke masa dangane da almubazzarancin kudade, inda ya bukaci ya bashi amsa cikin sa’o’I 24.

KU KARANTA: Sallah: An kashe bako a fadar Sarkin Kano, an jikkata da dama a hawan Daushe

Idan za’a tuna a ranar Litinin data gabata ne hukumar yaki da rashawa da sauraron koke koken jama’a ta jahar Kano ta kama Sarki Sunusi da laifin barnatar da kudi naira biliyan uku da miliyan dari hudu, har ma ta baiwa gwamna shawarar ya dakatar da Sarkin.

Shugaban ma’aikatan fadar Sarkin Kano, Munir Sunusi ya tabbatar da samun takardar da gwamnan Kano ya aiko ma Sarki ta hannun sakataren gwamnati, inda yace a ranar Alhamis takardar ta iso fada, kuma masarauta tana yin nazari game da takardar.

Bugu da kari rahotanni sun bayyana cewa a tuni gwamnatin ta kammala shirya kwamitin da za tayi nazarin duk amsar da Sarkin Kano ya baiwa gwamnati, inda ake sa ran kwamitin ne zata yanke hukuncin daya dace da Sarkin.

Sai dai majiyoyi daga fadar gwamnatin jahar Kano sun tabbatar da cewar duk ta kare Gwamna Ganduje zai yi awon gaba da rawanin Sarki Muhammadu Sunusi II ne, musamman tun bayan samun rahoton binciken hukumar yaki da rashawa ta jahar Kano a karkashin jagorancin Muhyi Magaji Rimin Gado.

Idan za’a tuna hukumar ta koka kan yadda wasu na hannun daman Sarkin guda hudu suka ki amsa gayyatar da tayi musu yayin da take gudanar da bincike akan zargin almubazzarancin, inda hukumar ta zargi Sarkin da hana mutanen nasa gurfana gaban hukumar.

A hannu guda kuma, Walin Kano ya musanta dukkanin tuhume tuhumen da ake yi ma Sarkin Kano da masarautar gabaki daya, inda yace masarautar Kano bata gaji naira biliyan 3.4 ba balle ma har ta almubazzarantar dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel