Da zafinsa: AU ta dakatar da kasar Sudan

Da zafinsa: AU ta dakatar da kasar Sudan

- Kungiyar kasashen Afurka ta AU ta dakatar da Sudan tare da cewa ba zata janye dakatarwar ba har sai an samu jagorancin farin hula a kasar.

- AU ta bada sanarwar wannan dakatarwar ne ta hanyar amfani da shafin sada zumuntar ta na twitter inda tace dakatarwar ta fara aiki da gaggawa.

Kungiyar hadin kan kasashen Afurka ta AU ta dakatar da kasar Sudan a ranar Alhamis kan kisan da jami’an sojin kasar su kayi wa masu zanga-zanga a kwanaki kalilan da suka gabata.

KU KARANTA: Bamu kori kowa daga aiki ba, inji gwamnati

Sashen kungiyar dake kula da tsaro da zaman lafiya ne ya bada sanarwar a shafin sada zumunta na twitter. “Mun dakatar da kasar Sudan daga kasancewa cikin kungiyar AU da gaggawa. Ba kuma zamu maido ta ba har sai an samu jagorancin farin hula wanda hakan ne kadai zai kawo karshen rikicin kasar.”

Sauran karin bayani kan lamarin na nan tafe…….

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel