Dalilin janye takara ta, inji Goje

Dalilin janye takara ta, inji Goje

- An samu fahimtar juna tsakanin sanata Lawan Ahmad da sanata Danjuma Goje

- Goje ya hakura da takararsa ya bar wa Lawan Ahmad sakamakon bukatar shugaba Buhari

- Wannan matsaya dai ta samu ne bayan an dau tsawon awa guda ana ganawa wacce ta samu halartar wasu muhimman mutane daga jam'iyar ta APC a villa dake Abuja.

Daya daga cikin wadanda ke kan gaba wurin neman kujerar shugabancin majalisar dattawa sanata Danjuma Goje ya bayyana dalilinsa na janye takararsa jim kadan bayan ganawarsa da shugaba Buhari ranar Alhamis a villa.

Goje wanda ya jogaranci kwamitin kasafi na majalisar dattawa ya janye takararsa bayan sunyi wata ganawa da shugaban kasa tare da abokin takararsa sanata Ahmad Lawan wanda shi ne APC ke goyon baya.

Bayan an kammala ganawar wacce a kwashi tsawon awa guda anayi, Goje ya ce ya janye takararsa bisa girmamawa ga shugaban kasa.

Bugu da kari, duk da yana ganin zai iya nasarar kawo wannan kujera ta shugabancin majalisar dattawa, Goje ya ce “dole na hakura ya janye saboda shugaban kasa ya sanya baki cikin lamarin.”

Wanda ya jagoranci zaman domin sasantawa tsakanin sanatocin biyu shi ne Mallam Nasir El-Rufai gwamnan jihar Kaduna.

KU KARANTA:Bamu kori kowa daga aiki ba, inji gwamnati

Har ila yau ganawar ta samu halartar babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan al’amuran majalisar dattawa sanata Ita Enang da kuma zababben sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Uba Sani.

Majalisar dokoki zata kaddamar da sabbin shugabannin ta a ranar Talata 11 ga watan Yuni, 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel