Saurayin da ya kone dangin budurwarsa zai fuskanci hukuncin kisa - Hukumar 'yan sanda

Saurayin da ya kone dangin budurwarsa zai fuskanci hukuncin kisa - Hukumar 'yan sanda

- Wani saurayi da ya kashe mutane takwas na dangin budurwar shi zai fuskanci hukuncin kisa

- Mutumin ya aikata laifin a watan Afrilun da ya gabata

- Bayan wannan mutumin ya taba kashe tsohuwar matarsa a shekarar 2000

Kwamishinan 'yan sandan jihar Ondo, Undie Adie, ya bayyana cewa Deji Adenuga, wanda ake zargi da sanyawa gidan budurwarshi wuta, inda mutane tara suke kwance suna bacci, kotu na tuhumar sa da kisan dangin budurwar tasa, da kuma tsohuwar matarsa da ake zargin ya kasheta ita ma.

A lokacin da yake magana da manema labarai a Akure babban birnin jihar yau Alhamis dinnan, kwamishinan ya ce mutumin wanda aka fi sani da Oluodo ya sanyawa dangin budurwar tashi wuta ranar 23 ga watan Afrilu, 2019 da misalin karfe 2 na dare.

KU KARANTA: An kai hari wani babban Masallacin Juma'a na kasar Jamus

Ya ce wanda ake zargin yanzu yana gidan yarin Olokuta dake garin Akure ya bayyana dalilin sa na sanya musu wutar, inda ya bayyana cewa akwai budurwarsa mai suna Titi Sanumi, wacce ya kashewa kudi masu tarin yawa sai tazo ta rabu dashi.

Kwamishinan ya ce mutane takwas daga cikin mutanen da suka kone din, wanda yawancin su yara ne sun mutu, inda budurwarshin ce kawai ta rage bata mutu ba wacce ke asibiti tana karbar magani.

Ya kara da cewa sai da suka sha wahala kafin daga baya suka kama wanda ake zargin ranar 28 ga watan Afrilu, 2019 a garin Ijebu Ode inda ya gudu bayan ya aikata lafin.

Ya bayyana mutumin a matsayin rikakken mai laifi da ya aika laifin kisa, bayan kuma ya taba kashe matarsa mai suna Abiye a shekarar 2000, inda a lokacin aka kai shi gidan yarin Olokuta.

Kwamishinan ya bayyana cewa Oluodo ya samu ya gudu daga gidan yarin a lokacin da aka fasa gidan yarin a shekarar 2013, ya kara da cewa za a yanke masa hukuncin wannan laifin da yayi da kuma wanda yayi a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel