Jagorancin majalisa: PDP ta karyata cewa tayi mubaya’a ga wasu yan takara

Jagorancin majalisa: PDP ta karyata cewa tayi mubaya’a ga wasu yan takara

- PDP ta karyata zarginta da ake na goyon bayan Femi Gbajabiamila na ya kasance kakakin majalisa ta 9

- Jam'iyar PDP ta watsi da wannan magana inda take cewa sam bata da dan takara ko daya wanda ta mara wa baya domin jagorancin majalisar

Yan jam’iyar PDP dake majalisar wakilai ta tarayya sun karyata maganar cewa sun yi mubaya’a ga Femi Gbajabiamila na ya kasance kakakin majalisa ta 9.

A wani zance da ya fito daga shugaban marasa rinjaye na majalisar Leo Ogor yace: “ wannan maganar gaba dayanta karya ce, yan majalisar PDP ba suyi mubaya’a ga Femi ko kuma wani dan takara ba na daban.”

Jaridar Daily Trust bata mance da zance batun jam’iyar PDP kan wanda tayi ranar Talata duk a bisa nuni ga ‘yan ‘yanta kan maganar wanda zasu goyi baya a matsayin kakakin majalisa ranar 11 ga watan Yuni da majalisar zata zabi sabbin shugabanni.

KU KARANTA:Bamu kori kowa daga aiki ba, inji gwamnati

Sai dai kuma abin ya dau salon tufka da warwara saboda zancen Ogor wanda ke cewa; “ A daidai lokacin da muke taya yan majalisa yan uwanmu musulmi murnar bikin karamar sallah, ya zama wajibi na tunatar da ku kan duk wata ganawa da zaku jam’iya ta kasance kan gaba ta yadda idan sun tattauna da yan takara zaku kawo mana bayani gabanmu.

“Akwai labarai na karya dake yawo a halin yanzu, wancan na ruwaito abu daban da wancan. Duba ga wannan jam’iyarmu bata baiwa kowa damar ya goyi bayan dan takarar APC ba. Ina sake tabbatar muku da cewa wannan magana da ake yadawa PDP ba ta san da ita ba.” A cewarsa.

Dan majalisar ya kara da cewa jiga-jigan PDP a majalisar na nan kansu hade har ila yau yayin da suke cigaba da sauraron masu takarar kakakin majalisar daya bayan daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel