Takun da Buhari ya kamata ya sauya a wa'adin sa na biyu - Lauyoyin Najeriya

Takun da Buhari ya kamata ya sauya a wa'adin sa na biyu - Lauyoyin Najeriya

Bayan samun nasara karo na biyu ta lashe babban zaben kasa da aka gudanar a watan Fabrairu, wasu zakakuran Lauyoyin Najeriya sun shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan sauya salon takun sa a wannan karo.

Domin tsananin kishin kasa da kuma fatan samun kyakkyawar makoma ta fidda kasar Najeriya zuwa tudun tsira, wasu manyan lauyoyin Najeriya sun shawarci shugaban kasa Buhari a kan zage dantsen sa wajen riko da akalar jagorancin kasar nan a karo na biyu.

A yayin da wasu daga cikin manyan lauyoyin kasar nan ke ci gaba da yiwa shugaban kasa Buhari fata na son barka gami da kyautata masa zato na inganta ci gaban kasar nan a wa'adin sa na biyu, wasu kuwa na ci gaba da sabanin haka.

Fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam Femi Falana, ya ce bai hango Najeriya akan tudun tsira ba kuma ba bu wani ci gaba da za a samu a kasar nan matukar shugaban kasa Buhari zai ci gaba da kasancewa a kan gado na mulkin kasar nan.

KARANTA KUMA: Shugaban 'yan sandan Najeriya ya nemi a tsaurara hukunci a kan masu garkuwa da mutane

Da yawa daga cikin lauyoyin sun nemi shugaban kasa Buhari da ya tashin tsaye wajen tabbatar da cika alkawurran da ya daukar wa al'ummar kasar nan a yayin yakin neman zabe na inganta tsaro, yaki da rashawa domin kwararar romon dimokuradiyya.

Cikin jerin shawarwari da manyan lauyoyin kasar nan suka nemi shugaban kasa Buhari da ya sauya takun sa wajen fidda A'i daga rogo sun hadar da;

1. Saukaka radadi na kangin talauci da ya yiwa kasar nan dabaibayi.

2. Habaka tattalin arziki da ke kan gabar durkushewa.

3. Samar da ayyukan yi musamman a tsakanin matasa

4. Inganta tsaro ta hanyar kawo karshen annobar ta'addanc da ya zamto ruwan dare a kasar nan.

5. Inganta ci gaban gine-gine da kuma wadatar wutar lantarki.

6. Tabbatar da yiwa doka da'a ba tare da nuna wariya ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel