An kashe shugaban kungiyar ISIS a Iraqi

An kashe shugaban kungiyar ISIS a Iraqi

Sojojin hadin gwiwa karkashin jagorancin kasar Amurka sun kashe wani shugaba a kungiyar ISIS a daren Laraba sakamakon luguden wuta da su kayi da jiragen sama a yunkurin su na kakkabo sauran 'yan ta'addan da su kayi saura a yankin.

Tun bayan da aka ci gabala kan kungiyar a Iraqi da Syria, 'yan ta'addan sunyi kwanton bauna inda suka kai hare-hare a kasashen da ke makwabtaka da Iraqi da Syria domin yadda manufar su.

"Harin jiragen sama da aka kai a mabuyar 'yan ta'addan ya yi sanadiyar mutuwar 'yan ta'adda 6 ciki har da Sarkin Wiliayar Al Jazeera, Abu Musallam Al Iraqi da motoccin su guda biyu," inji kwamandan dakarun 'yan asalin kasar da ke Anbar, Qatary Al Samarmad.

DUBA WANNAN: Sojoji sunyi luguden wuta a sansanin Boko Haram da ke Tumbun Kaiyowa

An kai harin ne a tsibirin Tharthar da ke Arewa maso Yammacin Baghdad.

Harin na cikin wani hadin gwiwa na tsaro da akayi tsakanin sojojin Iraqi da kabilun da ke zaune a yankin domin yaki da kungiyar 'yan ta'addan, inji Mista Al Samarmad.

Gamayar dakarun sojojin Iraqi tare da sojojin Amurka da aka kafa domin yaki da ISIS sun mayar da hankalinsu kan wuraren da ake tsamanin 'yan ta'addan sun koma domin samun mafaka.

An kafa gamayyar sojojin ne bayan ISIS ta mamaye garuruwa masu yawa a yankin.

ISIS suna ta karfi a kauyukan Iraqi musamman wadanda ke kebe wanda hakan ke ba su damar shirya hare-hare.

Ab tabbatar da cewa 'yan kungiyar na ISIS sun yada zango a wurare kamar yankin sahara na Anbar da Nineveh da kuma tsibirin Kirkuk, Salah Al Din da Diyala.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel