Masari ya gamsu cewa jami’an soji za su kawo karshen ta’addancin ‘yan baranda

Masari ya gamsu cewa jami’an soji za su kawo karshen ta’addancin ‘yan baranda

- Aminu Masari ya nuna goyon bayansa ga jami'an soji inda yake cewa hakika zasu ga bayan yan bindiga dake yankin arewacin kasar nan

- Gwamnan yayi wannan jawabin ne yayin da babban hafsun sojin Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai ya kai masa ziyara a fadar gwamnatin jihar Katsina

- Masari yace al’amarin yan bindigan dake addabar jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi da wani bangaren Kaduna bai da alaka da addini ko kadan

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana kyakkyawan zatonsa ga rundunar sojin Najeriya kan cewa za tayi nasara wurin murkushe ‘yan bindiga, masu kisa da kuma garkuwa da bil adama a wasu jihohin kasar nan.

Masari ya yi wannan furucin ne yayin da ya karbi bakuncin hafsun sojin Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai a fadar gwamnatin Katsina.

Gwamnan ya ce, “Tunda dai jami’an soji tare da takwarorinta su kayi nasarar gamawa da Boko Haram a Arewa maso Gabashin kasar nan to tabbas zata iya ganin bayan ‘yan baradan.

“Hakika zaku ga bayan wadannan yan ta’addan dake takura mutane ta hanyar sanya su cikin halin wayyo ni Allah. A gani na kuna da kwarewa da fasahar yaki domin magance ire-ire wadannan matsaloli.

“Mu ba zamu zuba idanu ba ana kashe jama’ar Katsina ba. Ya zama wajibi a garemu mu dauki mataki mafi dacewa da wannan al’amari.”

KU KARANTA: Mutum 6 da aka sace a Taraba sun kai wata biyu a tsare yanzu

Kazalika gwamnan yayi karin haske kan cewa al’amarin yan bindigan dake addabar jihohin Zamfara, Sokoto, Kebbi da wani bangaren Kaduna bai da alaka da addini ko kadan.

Gwamnan ya sake bayar da tabbacin zai bada gudumawa ga jami’an tsaro domin yaki ta’addanci a jiharsa, duba ga yadda kariyar dukiyoyi da rayukan jama’a ke da matukar muhimmanci.

“ Ya zama wajibi a garemu na mu bada kariya ga dukiya da kuma rayukan jama’a a matsayinmu na gwamnati. A don haka zamu cigaba da yin abinda muka riga muka saba ba tare da gajiyawa ba,” inji gwamnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel