Yanzu Yanzu: Shugabancin majalisar dattawa: Goje ya janye daga tseren ya mara wa Lawan baya

Yanzu Yanzu: Shugabancin majalisar dattawa: Goje ya janye daga tseren ya mara wa Lawan baya

- Sanata Danjuma Goje ya janye daga tseren takarar kujerar Shugaban majalisar dattawa bayan ganawa da shugaban kasa Buhari

- Goje ya jadadda goyon bayansa ga Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya bayyana hkan ga manema labarai a yau Alhamis 6 ga watan Yuni

Bayan ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni, Sanata Danjuma Goje ya janye daga tseren takarar kujerar Shugaban majalisar dattawa.

A yanzu dai Goje ya jadadda goyon bayansa ga Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan domin darewa kujerar.

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ne ya bayyana hakan bayan ganawr sirri da suka yi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamna El-Rufai ya kasace tare da Sanata awan, Sanata Goje, da kuma babban mai ba Shugaban kasa shawara akan harkokin majalisar dokoki, Sanata Ita Enang a yayinda yake jawabi ga manema labarai na fadar Shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Hawan Sallah: Yan sanda sun kama yan daba 10 a Kano

Yan majalisar dokoki kasar za su gudar da zabe domin maye gurbin Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da wani a ranar 11 ga watan Yuni.

Tun da fari dai shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun nuna goyon bayansu ga Lawan a matsayin wanda suke so ya zama Shugaban majalisar dattawan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel