Shugaban 'yan sandan Najeriya ya nemi a tsaurara hukunci a kan masu garkuwa da mutane

Shugaban 'yan sandan Najeriya ya nemi a tsaurara hukunci a kan masu garkuwa da mutane

Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya Muhammadu Adamu, ya yi kira na neman a tsaurara hukunci kan masu ta'addancin garkuwa da mutane musamman kwace dukkanin kadarar wadanda aka samu da wannan mummunar ta'ada.

Tuni dai wasu jihohin tamkar Zamfara da kuma Edo sun shar'anta hukuncin kisa kan duk wani mai ta'addancin garkuwa da mutane da ya shiga hannu.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya Frank Mba ya bayyana, sufeto janar na 'yan sandan kasar nan ya yi wannan kira ne yayin karbar gaisuwar sallah ta tawagar kungiyar kananan hukumomin Najeriya reshen jihar Nasarawa bisa jagorancin Aminu Maifata da ta ziyarci ofishin sa dake garin Abuja.

Shugaban hukumar 'yan sandan kasar nan ya jaddada cewa wannan kira na da muhimmancin gaske duba da yadda ta'addancin masu garkuwa da mutane da kuma wasu nau'ikan ta'addanci daban daban da suka zamto ruwan dare a fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: An nemi Buhari ya shiga tsakanin rikicin Oyegun da Oshiomhole

A yayin kyautata zaton sa kan yadda tabbatuwar wannan kira na tsaurara hukunci zai magance ta'addanci a kasar nan, babban sufeton na 'yan sanda ya ce a halin yanzu masu ta'adar garkuwa da mutane 63 sun shiga hannu tun yayin kaddamar da gudanarwar su mai lakabin Operation Puff Adder a ranar 5 ga watan Afrilu.

Kazalika tun daga wannan lokaci kamar yadda babban sufeton ya bayar da shaida an kama miyagu 2,175 masu zartar da wasu nau'ikan ta'addanci daban daban da suka hadar da fashi da makami, kisan gilla, da kuma 'yan kungiyoyin asiri.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel