Yanzu Yanzu: Sanata Lawan da Goje na cikin ganawar sirri da Buhari

Yanzu Yanzu: Sanata Lawan da Goje na cikin ganawar sirri da Buhari

A yanzu haka manyan yan takarar kujerar Shugaban majalisar dattawa biyu, Ahmed Lawa daga jihar Yobe da Danjuma Goje daga jihar Gombe a cikin ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ofishinsa.

Sanatocin biyu sun isa fadar Shugaban kasa a tare 11:00 da yan mintuna na safe, sannan kai tsaye suka wuce ofishi Shugaban kasar.

Sun zo jim kadan bayan Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya isa fadar Shugaban kasar sannan ya doshi ofishin Shugaban kasar.

Ganawar nasu baya rasa nasaba ga amen Sanata Goje ya janye daga tseren domin ba Lawan damar darewa kujerar.

Yan majalisar dokoki kasar za su gudaar da zabe domin maye gurbin Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da wani a ranar 11 ga watan Yuni.

Da farko dai shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun nuna goyon bayansu ga Lawan a matsayin wanda suke so ya zama Shugaban majalisar dattawan.

KU KARANTA KUMA: Kasar Saudiyya ta kwararo ruwan yabo ga Buhari kan zabar Bende a matsayin Shugaban UNGA

Rahotanni sun kuma nuna cewa hakan na iya juyewa akan Goje saboda yana da goyon bayan wasu sanatocin APC da na jam’iyar adawa.

Mista Lawan a kasance Shugaban masu rinjaye a majalisa yayinda Goje ya kasance sugaban kwaitin kasafi kudi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel