Bamu kori kowa daga aiki ba, inji gwamnati

Bamu kori kowa daga aiki ba, inji gwamnati

- Gwamnatin jihar Kwara tayi watsi da jita-jitar dake yawo cewa ta sallami ma'aikatan da tsohuwar gwamnatin jihar ta dauka aiki tana daf da barin mulki.

- Hadimin gwamna Abdulrahman mai taimakamasa akan harkokin labarai ne yayi karin hasken kan lamarin a ranar Alhamis inda ya sanar da yan jarida hakikanin gaskiyar lamarin.

Gwamnatin jihar Kwara ta karyata zancen dake yawo cewa ta sallami ma’aikatanta inda tace ko kadan wannan batun ba gaskiya bane.

A wani zance da ya fito daga hannun hadimin gwamna Abdulrahman Abdulrazak mai kula da sashen labarai, Agboola Olarewaju ya ce, “ Karyane gwamnatin Abdulrahman Abdulrazak bata kori ma’aikaci ko guda ba daga aiki.”

KU KARANTA:Mutum 6 da aka sace a Taraba sun kai wata biyu a tsare yanzu

Zance wanda gwamnati ta fitar yayi karin haske akan ma’aikatan da gwamnati da ta shude ta dauka aiki. Dalilin rashin albashi da ba’a biya wasu daga cikin ma’aikatan ba kuwa ya samo asali daga wata munakisa yayin daukarsu aiki.

A cewar hadimin: “ Akasarin wadannan ma’aikatan ba su samu tantancewa ba daga wurin gwamnati domin biyansu albashi. An dauke su aiki ne a cikin watan Mayu don haka babu yadda za’ayi su samu albashin wannan watan.”

“ Irin wannan daukar aiki shi ake kira bayar da aiki da yammaci, bi ma’ana gwamnati na shirin barin mulki sai kuma ta dauki sabbin ma’aikata.

“A maimaikon sallamar ma’aikatan sai bamuyi haka ba, muka duba takardunsu da kuma cancantarsu domin tabbatar da cewa sun dace da wuraren da aka kai su.

“A jihohin Ogun, Bauchi da wasu jihohin sallamar irin wadannan ma’aikatan akayi saboda nauyi zasu zamewa sabuwar gwamnati,” inji Olarewaju.

Olarewaju ya sake jaddadawa cewa “babu ma’aikaci ko guda daya da aka kora, albashin da suke bi kuma zai iso zuwa garesu bayan an yi binciken da ya dace kan daukarsu aikin da akayi.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel