An samu daruruwan butocin alwala da suka bata a cikin wata bishiya (Bidiyo)

An samu daruruwan butocin alwala da suka bata a cikin wata bishiya (Bidiyo)

Akwai wani bidiyo da ke yaduwa a kafafen sada zumunta da ke nuna wasu 'yan uwa musulmi da suka sare wata bishiya kuma su ka gano abinda ya ba su mamaki.

Wani fitaccen jarumin Nollywood kuma mai shirya fina-finai Ernest Obi ya wallafa bidiyon da masoyan sa a shafinsa na Instagram.

A rubutun da ya wallafa, Mai shirya fina-finan ya ce idan da a cikin fim ne wannan abin ya faru, wasu mutane za su yi suka da cewa hakan ba zai taba faruwa ba.

Ya kara da cewa an gano daruruwan butoci na alwala da suka bace daga masallaci a cikin bishiyar.

DUBA WANNAN: Fittacen malamin Najeriya ya yi rabon kayan tallafi ga al'umma a masallacin Makkah

Bidiyon da Obi ya wallafa ya nuna wasu masallata suna sare wata bishiya da zarto mai inji yayin da wasu suka tsaya a gefe guda suna kallon ikon Allah.

Kafin a gama sare bishiyar, wani mutumi ya fara ciro butoci masu dimbin yawa da suka shige cikin bishiyar. Kalli faifan bidiyon a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel