Hawan Sallah: Yan sanda sun kama yan daba 10 a Kano

Hawan Sallah: Yan sanda sun kama yan daba 10 a Kano

Rundunar yan sandar jihar Kano sun kama akalla yan daba 10, biyo bayan mumunan karo da aka yi wanda ya kai da zub da jini a lokacin hawan Sallah a birnin jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ta rahoto cewa an gudanar da al’adar ‘Hawan Daushe’ a fadar mai martaba sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II, duk daga cikin bukuwan karamar Sallah.

Kakakin rundunar yan sanda, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da lamarin a jawabin da ya gabatar a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni.

Haruna ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni bayan bikin hawan daushe inda yan daban suka tayar da tarzoma wanda hakan yayi sanadiyar barkewar fadace fadace.

Kakakin rundunar, har ila yau, ya kara da cewa an soma gudanar da bincike akan lamarin.

Haruna ya bayyana cewa za’a gurfanar masu laifin da aka kama da makamai bayan an kammala bincike.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un: 'Yan bindiga sun harbe mutane 16 a jihar Zamfara yayin da ake gabatar da bikin sallah

A baya Legit.ng ta rahoto cewa rikici ya barke a kofar fadar da misalin karfe 7 na dare yayin da aka kammala gudanar da hawan Sallah, sakamakon wasu kungiyoyin matasa masu hamayya da juna da suka far ma kawunansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel