Kasar Saudiyya ta kwararo ruwan yabo ga Buhari kan zabar Bende a matsayin Shugaban UNGA

Kasar Saudiyya ta kwararo ruwan yabo ga Buhari kan zabar Bende a matsayin Shugaban UNGA

- Jakadan kasar Saudiyya a Najeriya, Adnan Bostaji, ya bayyana zabar Farfesa Tijjani Mohammed-Bande a matsayin Shugaban UNGA a matsayin Karin daraja ga diflomasiyyar kasar Najeriya

- Jakadan na kasar Saudiyya yace zaben babban nasara ce wacce gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cancanta

- Bostaji ya kara da cewa zaben godiya ne ga martabar Najeriya a tsakanin kasashen duniya da kuma rawar ganin da take takawa akan lamuran da suka shafi kasashe

Jakadan kasar Saudiyya a Najeriya, Adnan Bostaji ya bayyana zaben Farfesa Tijjani Mohammed-Bande a matsayin Shugaban majalisar dinkin duniya (UNGA) a matsayin Karin daraja ga diflomasiyyar Najeriya.

Bostaji yayi sharhin ne a wani jawabi da aka saki a Abuja a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, jaridar The Nation ta ruwaito.

Legit. ng ta tattaro cewa jakadan Saudiyyan yace nasarar Bande abun alfahari ne da kuma farin ciki ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ku tuna a baya cewa Legit.ng ta rahoto a baya cewa Farfesa Tijjani Mohammed Bande, tsohon shugaban jami'ar Usman Danfodiyo dake Sokoto, ya zama sabon shugaban majalisar wakilan dinkin duniya (UN).

KU KARANTA KUMA: Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un: 'Yan bindiga sun harbe mutane 16 a jihar Zamfara yayin da ake gabatar da bikin sallah

Tun kafin tabbatar da nadinsa, shugabar majalisar mai barin gado, Maria Fermanda Espinosa Garces, ta bayyana cewar Bande na kan hanya dodar domin zama sabon shugaban majalisar wakilan UN.

Ta bayyana hakan ne yayin wata gana wa da da tayi da shugaba Buhari da ministansa na harkokin kasashen ketare a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel