Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un: 'Yan bindiga sun harbe mutane 16 a jihar Zamfara yayin da ake gabatar da bikin sallah

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un: 'Yan bindiga sun harbe mutane 16 a jihar Zamfara yayin da ake gabatar da bikin sallah

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe mutum 16 a yankin Kanoma da ke karamar hukumar Maru da ke Zamfara a ranar Sallah.

Da yake tabbatar da lamarin a wani jawabin manema labarai a Gusau a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, Darakta Janar labaran gwamnan jihar, Yusuf Idris yace: “gwamnan ya ziyarci garin domin yi masu jaje.

“A lokacin ziyarar, gwamnan ya kuma umurci hukumomin tsaro da su yi gaggawan shiga aiki domin kamo wadanda suka aikata ta’asar.

“Gwamnan ya kuma umurci dauke mutum 14 da suka ji rauni sakamakon harbin bindiga daga babbar asibitin Kanoma, zuwa cibiyar kiwon lafiya na tarayya, Gusau domin samun ingantaccen kula.

“Gwamnatin jihar ce za ta dauki nauyin biyan kudin asibitin,” inji shi,.

Ya kuma bayyana cewa gwamnan jihar ya yanke shawarar hada hannu da duk wasu mutane da kungiyoyi domin kawo karshen ta’addanci a jihar.

KU KARANTA KUMA: Wasu masu fada aji a kasar nan sun bukaci Kotu ta tsige Buhari saboda ya bai wa INEC takardun karya

Yace hakimin Kanoma, Yahaya Mohammed, ya fada ma gwamnan cewa yan bindigan sun kai mamaya yankin ne da yamma sannan suka fara harbi ba kakkautawa, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum 16 da raunata wasu 14.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel