Wasu masu fada aji a kasar nan sun bukaci Kotu ta tsige Buhari saboda ya bai wa INEC takardun karya

Wasu masu fada aji a kasar nan sun bukaci Kotu ta tsige Buhari saboda ya bai wa INEC takardun karya

Wasu yan Najeriya uku sun bukaci kotun daukaka kara da ke Abuja da ta nuna rashin cancantar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takara a zaben Shugaban kasa da aka gudanar kwanaki kan zargin gabatar da takardun karya ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Rokon na kunshe ne a wani kara da suka daukaka aka hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja wacce ta kori kararsu a ranar 2 ga watan Mayu.

Masu karar sune Kalu Agu, Labaran Ismai’l da kuma Hassy El-Kuris.

Sun bukaci kotu da ta kaddamar da cew Buhari ya gabatar da bayanan bogi game da karatunsa ga INEC domin takarar zaben Shugaban kasa a 2019.

Sun nemi wani umurni da zai hana Buhari gabatar da kansa a matsayin dan takara a zaben Shugaban kasa.

Sun bukaci wani umurni da zai sa APC ta tsige sunan Buhari a matsayin dan takarar jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun kashe mahaifiyar wata tsohuwar yar majalisa

Sai dai hukuncin da aka yanke a ranar 2 ga wata Mayu, Justis Ahmed Mohammed na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya kori karar kan cewa ba a shigar dashi a lokacin da kundin tsarin mulki ta tanadar ba.

Don haka a yanzu suka daukaka kara akan hukuncin da kotun tarayya ta zartar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel